in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mataimakin babban magatakardan MDD ya yi bayani kan ziyararsa a Koriya ta Arewa
2017-12-10 13:41:53 cri
Jiya Asabar, mataimakin babban magatakardan MDD mai kula da harkokin siyasa Jeffrey Feltman, ya yi bayani kan ziyararsa a kasar Koriya ta Arewa, inda ya jaddada babbar bukata ta sassauta yanayin siyasa a zirin Koriyar, da kuma muhimmancin warware matsalar ta hanyar siyasa.

A ranar 8 ga wata, Mista Feltman ya kammala ziyarar aikinsa a Koriya ta Arewa na kwanaki 4, sa'an nan, ya bayyanawa kafofin watsa labarai cewa, ba za a sassauta yanayin siyasa a zirin Koriya ba, sai ta hanyar diflomasiyya da kuma yin shawarwari yadda ya kamata. Haka kuma, ya kamata a dauki matakai cikin sauri ta yadda za a iya warware matsalar.

A yayin ziyarar tasa a kasar Koriya ta Arewa tun daga ranar 5 zuwa ranar 8 ga wata, ya jaddada muhimmancin aiwatar da kudurin da kwamitin sulhu na MDD ya tsaida bisa dukkan fannoni. A sa'i daya kuma, ya bayyana cewa, ya kamata a yi mu'amala da bangarori daban daban da abin ya shafa domin magance rikice-rikicen da bai kamata ba. Haka kuma, gamayyar kasa da kasa sun nuna damuwa sosai kan tabarbarewar yanayin siyasa a zirin Koriyar a halin yanzu, inda kuma suka dukufa wajen warware matsalar cikin lumana. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China