in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta ki amincewa da daftarin da kwamitin sulhun MDD ya gabatar game da matsayin birnin Kudus
2017-12-19 11:11:51 cri
A jiya Litinin ne, kasar Amurka ta kada kuri'ar kin amincewa da daftarin da kwamitin sulhun MDD ya gabatar game da batun matsayin birnin Kudus.

A wannan rana, kwamitin sulhun MDD ya jefa kuri'u kan wani daftari da kasar Masar ta gabatar don nuna kin amincewa da kudurin kasar Amurka na amince da birnin Kudus a matsayin babban birnin kasar Isra'ila, inda aka samu kuri'un goyon baya 14 da kuma kuri'ar ki amincewa 1. Yanzu dai ba za a zartarsa wannan kuduri ba, Saboda matsayin kasar Amurka na kasa mai wakilicin din-din-din a kwamitin sulhun MDD wadda ta ki amincewa da daftarin.

Bayan kammala jefa kuri'un, mukaddashin wakilin kasar Sin dake MDD Wu Haitao ya bayyana cewa, batun Palesdinu muhimmin batu ne a yankin gabas ta tsakiya, kuma shi ne kashin bayan shimfida zaman lafiya a yankin. A don haka, ya kamata kwamitin sulhun MDD da sauran kasashen duniya su hada kai wajen ganin an sassauta matsalar birnin Kudus tare da tabbatar da zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya gaba daya.

A ranar 6 ga wannan wata ne, Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ayyana birnin Kudus a matsayin babban birnin Isra'ila, tare kuma da dawo da ofishin jakadancin Amurka dake kasar Isra'ila daga birnin Tel Aviv zuwa birnin Kudus. Kasashen duniya dai sun ki amincewa da wannan mataki na Amurka. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China