A ranar Laraba ne tawagar kiyaye zaman lafiya ta Amurka dake kungiyar tarayyar Afrika da kuma AU suka kaddamar da wani taron kwanaki 3 mai taken kawar da tashin hankali na masu tsattsauran ra'ayi (CVE) a helkwatar kungiyar tarayyar Afrika dake Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha.
Jessica Davis Ba, mataimakiyar babban jami'in shirin wanzar da zaman lafiya na Amurka a AU, ta yi alkawarin cewa, Amurkar za ta hada gwiwa da AU domin kawo karshen aukuwar munanan al'amurra makamancin wanda ya faru a Mogadishu ko kuma kamar harin da aka kaddamar a kasar Masar.(Ahmad Fagam)