Sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen Sudan din ta fitar ta bayyana cewa, shugaban na AU zai fara ziyarar tasa ne da tattauanwa da ministan harkokin wajen kasar Ibrahim Ghandour,.
A cewar sanarwar, tattauanwar jami'an zata mayar da hankali ne kan halin da ake ciki a kasar ta gabashin Afrika da kuma sauran batutuwa da suka shafi nahiyar Afrika.
Mahamat zai kuma gana da shugaban Sudan Omar al-Bashir da firaiministan kasar Bakri Hassan Saleh.