in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta bayyana takaici game da halin da 'yan ci ranin Afrika ke ciki a Libya
2017-11-20 11:05:39 cri
Shugaban hukumar Tarayyar Afrika AU Moussa Faki Mahamat, ya bayyana takaici game da rahoton da ya samu, dake cewa ana sayar da 'yan ci ranin Afrika a matsayin bayi a Libiya.

Sanarwar da AU ta fitar, ta ce shugaban ya yi soki dabi'ar da kakkausar murya, inda ya ce ta saba da akidu mazan jiya da suka kafa tarayar da ma manufofin nahiyar da na kasa da kasa, ciki har da hukumar kare hakkin dan Adam ta Afrika.

Shugaban ya yi kira da a kawo karshen dabi'ar da sauran laifukan da suka shafi safarar bil'adama nan take.

Ya kuma bukaci a gaggauta zakulo dukkan wadanda ke da hannu da abokan huldarsu, domin su fuskanci hukunci.

Game da haka ne ya yi maraba da sanarwa da hukumomin Libya suka bayar, na gudanar da bincike kan al'amarin, inda ya ke fatan za a samu sahihin sakamako.

Har ila yau, Moussa Faki Mahamata ya bukaci hukumomin su yi dukkan abun da za su iya wajen ganin sun inganta yanayin da 'yan ci ranin Afrika dake kasar suke ciki.

Shugaban na AU ya kuma bayyana kudurin Tarayyar na yin dukkan mai yiwuwa wajen ganin an kawo karshen al'amarin tare da tabbatar da mutunta hakkokin bil adama. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China