in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta kaddamar da shirin yaki da cin zarafin mata a Somalia
2017-11-26 13:28:14 cri
Shirin wanzar da zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afrika a Somaliya (AMISOM), ya kaddamar da shirin yaki da cin zarafi da muzgunawa mata da 'yan mata a kasar ta gabashin Afrika.

Shirin mai taken kwanaki 16 na gwagwarmayar yaki da cin zarafin mata na cikin gida, an kaddamar da shi nan take a sassan babban birnin kasar ta Somalia, a matsayin wani shirin wayar da kan al'umma na kasa da kasa game da wasu batutuwa da suka shafi take hakkin bil adama.

Da take jawabi a lokacin kaddamar da shirin a Mogadishu, Christine Alalo, mataimakiyar kwamishinan 'yan sandan AMISOM, ta bukaci wadanda aka ci zarafinsu a kasar da su fito fili su bayyana irin nau'in keta haddin da aka aikata musu.

Taken bikin na wannan shekara shi ne "babu wanda za'a bari a baya a fagen yaki da cin zafin mata da 'yan mata"

Tace, AMISOM a shirye take ta kawo karshen cin zarafin mata da 'yan mata wanda ya kasance a matsayin wani nau'i na nuna bambanci mafi girma.

Shirin gwagwarmayar yaki da cin zarafin jinsin na kwanaki 16, ana shirya shi ne a duk shekara a fadin duniya, wanda aka fara gudanarwa a ranar 25 ga watan Nuwambar kowace shekara a matsayin ranar yaki da cin zarafin mata ta kasa da kasa, kana aka kawo karshensa a ranar 10 ga watan Disamba ne ake gudanar da bikin ranar 'yancin adam ta duniya.

A cewar rahoton MDD na shekarar 2016, bisa alkaluman da aka samu daga kasashen duniya 87, kashi 19 bisa 100 na mata wadanda shekarunsu ya kai daga 15 zuwa 49, sun taba fuskantar wani nau'i na cin zafari ko muzgunawa na zahiri ko kuma cin zarafi ta hanyar yin lalata dasu.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China