Smail Cherguyi wanda ya bayyana hakan yayin da ya ke jawabi a taron tuntuba na MDD da AU karo 11 game da magance aukuwar rigingimu, ya ce kungiyar AU za ta sanya ido kan wadannan zabuka da za a gudanar a shekarar 2018 yadda ta kamata.
Kwamishinan ya ce, duk da fargabar da ake, ana saran gudanar da galibin wadannan zabuka cikin lumana. A cewarsa, kungiyar tarayyar Afirka, za ta sanya ido kan zabukan da za a gudanar a kasashen Masar, Mali, Saliyo da Togo. Sauran sun hada da Guinea Bissau, Madagascar da Jamhuriyar demokirayar Congo da kuma Zimbabwe.(Ibrahim)