in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban AU ya fara ziyarar aiki a Afrika ta Kudu don tattaunawa game ciniki mai 'yanci a nahiyar
2017-10-31 10:32:07 cri
Shugaban kungiyar tarayyar Afrika AU, Moussa Faki Mahamat, a ranar Litinin ya fara ziyarar aiki ta kwanaki biyu a kasar Afrika ta Kudu domin tattauna wasu batutuwa ciki har da batun kasuwanci mai 'yanci a tsakanin nahiyar wato (CFTA) a takaice.

Wata sanarwa da kungiyar tarayyar Afrikan ta fitar ta nuna cewa, shugaban na AU zai gana da shugaban kasar Afrika ta kudu Jacob Zuma, da ministan hulda da kasashen waje na Afrika ta Kudun, Maite Nkoana-Mashabane, da kuma sauran manyan kusoshin gwamnatin kasar.

Tattaunawar da za su gudanar za ta fi mayar da hankali ne kan batun hanyoyin da za'a bi don magance tashe tashen hankula a nahiyar, da kuma batun yadda za'a habaka tattalin arziki da samar da ayyukan raya kasashen nahiyar, sai kuma batun yadda za'a aiwatar da harkokin cinikayya cikin 'yanci a nahiyar, da cimma matsaya guda game da sha'anin sufurin jiragen sama a tsakanin kasashen nahiyar, sai kuma batun kyautata tsarin kimiyya a jami'o'in nahiyar ta Afrika.

A cewar sanarwar da aka fitar ta ambato cewa, jami'in na AU zai tattauna da hukumomin kasar Afrika ta Kudun game da cigaban da aka samu wajen aiwatar da shirin yin kwaskwarima kan manufofin kungiyar ta AU wanda aka amince da su a taron kolin kungiyar a Addis Ababa a watan Janairun shekarar nan ta 2017.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China