Alkaluma na nuna cewa, Sinawa masu yawon bude ido da suka ziyarci kasar a shekarar da ta gabata ya karu a kan Sinawa 41,659 da suka ziyarci kasar a shekarar 2015.
Da yake Karin haske darektan hulda da jama'a da harkokin kasa da kasa a ma'ikatar al'adu da yawon shakatawa na kasar Habasha Gezahegn Anate, ya ce duk da karuwar Sinawan dake kawo ziyara kasar a shekaru da dama da suka gabata, karancin abinci da wuraren kwana na kara kawo nakasu ga masu sha'awar zuwa yawon shatakawa kasar.
Abate ya ce, Sinawa ne na uku dake kawo ziyara kasar, bayan Amurkawa da 'yan kasar Burtaniya. A don haka ma'aikatar al'adu da harkokin yawon shakatawa ta kasar, tana karfafawa Sinawa gwiwar zuba jari a bangaren yawon shakatawa, da nufin kara janyo Sinawa masu yawon bude ido a kasar.
Yanzu haka dai kasar Habasha tana shirin aiwatar da wasu matakan rangwame ga 'yan kasuwa da ke harkokin yawon bude ido da bangaren samar da hidima, ciki har da shirin cire haraji kan kayayyakin gine-gine,ta yadda harkar yawon bude ido za ta kasance babbar kafa da kasar za ta rika samun kudaden ketare.(Ibrahim)