in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Habasha: 'Yan ta'adda 156 sun mika wuya a cikin watanni 4 da suka gabata
2017-12-15 09:28:12 cri

Gwamnatin kasar Habasha ta bayyana cewa, wasu 'yan ta'adda su 156 sun mika wuya ga hukumomin tsaron kasar cikin watanni 4 da suka gabata.

Wata kafar watsa labaran kasar ta ruwaito cewa, 'yan ta'addan sun kunshi magoya bayan kungiyoyi kamar su Ginbot-7, da Oromo Liberation Front (OLF), da Amhara People's Democratic Movement (APDM), da na Tigray People's Democratic Movement (TPDM).

Da yake karin haske game da hakan, mataimakin babban jami'in tsaron yankin yammacin Tigray Teku Meteko, ya ce wadanda suka mika wuyan, na samun mafaka ne a kasar Eritrea mai makwabtaka da Habasha.

Mr. Meteko ya ce sama da magoya bayan kungiyoyin 'yan ta'adda 160 ne suka koma gida Habasha cikin shekarar nan dake daf da karewa.

Habasha dai na zargin makwabciyarta Eritrea da tallafawa masu tada kayar baya a kasar, yayin da ita kuma Eritrea ke zargin Habashan da taimakawa 'yan tawayen dake adawa da ita, tare da kitsa wani shiri na mayar da ita saniyar ware tsakanin kasashen duniya.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China