Da yake jawabi a lokacin bikin bada lambar yabo kan sha'anin fasahar kirkire kirkire na kasar wato NSTIA a Addis Ababa babban birnin kasar, Desalegn ya ce, karfafa gwiwa kan fasahar kirkire-kirkire zai yi matukar bunkasa ci gaban tattalin arzikin kasar.
Da yake nuna muhimmancin da gwamnatin kasar ke bayarwa game da sha'anin kirkire-kirkire, firaiministan ya bayar da lambar yabo ta zinare kimanin 29, da azurfa 50, da kuma tagulla 66 ga wasu 'yan kasar da suka yi fice kan fasahar kirkire-kirkire su 145, da suka hada da dalibai da masu bincike, da kuma malaman makaranta sakamakon irin gudummawar da suka bayar a fannin ci gaban fasahar sadarwa ta zamani a kasar ta Habasha.
Ya kara da cewa, a yayin da kasar Habasha ke kokarin bunkasa ci gaban tattalin arzikinta, akwai bukatar karfafa gwiwa a fannin fasahar sadarwa ta zamani domin samun karin nasarori. (Ahmad Fagam)