in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tashin hankali a Oromia na kasar Habasha ya yi sanadin rayuka 11
2017-10-23 16:19:55 cri
Tashin hankali da ya barke a jihar Oromia na kasar Habasha, ya yi sanadin mutuwar mutane 11 a kwanakin baya-bayan nan.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwar da Kakakin jihohin Oromia da Amhara suka wallafa a shafinsu na facebook game da tashin hankalin da aka shafe mako guda ana yi, wanda kuma ya haifar da cikas ga harkokin kasuwanci tare da kone-kone a wasu wurare daban-daban.

Kakakin Oromia Addisu Arega, ya ce a yanzu al'amura sun daidaita, kuma an kama mutanen da ake zargi da haddasa rikicin.

A nasa bangaren, kakakin Amhara Nigusu Tilahun cewa ya yi, rikicin ya raba mutanen da har yanzu ba a san adadinsu ba da muhallansu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China