Workneh Gebeyehu, ya yi wannan kira ne a lokacin ganawa da sabon jakadan kasar Sin a Habasha, Tan Jian. A ranar Litinin ne ministan ya karbi takardar kama aiki na sabon jakadan na Sin. A cewar Gebeyehu, dangantakar dake tsakanin Sin da Habasha tana kara kyautatuwa a 'yan shekarun da suka gabata. Gebeyehu ya jaddada bukatar zurfafa dangantakar tattalin arziki tsakanin kasashen biyu zuwa babban mataki. (Ahmad Fagam)