in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnan Sokoto ya bukaci a haramta amfani da maganin Codeine a kasar
2017-12-20 10:44:53 cri

Gwamnan jihar Sokoto dake arewa maso yammacin kasar Najeriya ya bukaci gwamnatin tarayya ta haramta ta'ammali da maganin tari na ruwa na Codeine a duk fadin kasar.

Gwamna Aminu Tambuwal, ya bayyana hakan ne a birnin Kano a lokacin da yake gabatar da jawabi a wani taron dandali da aka shirya game da dakile amfani da abubuwan dake sa maye, ya ce ya zama tilas a haramta amfani da maganin tarin na Codeine saboda yadda ake amfani da shi ba bisa ka'ida ba inda matasa ke amfani da shi a matsayin abin da ke sa maye.

Taron na wuni biyu wanda majalisar dattijai kasar ta shirya a matsayin daya daga cikin matakan kawo karshe amfani da magunguna da kwayoyi dake bugarwa a fadin kasar, a kokarin kawo karshen matsalar da ta addabi kasar.

Gwamnan ya ce, ya zama tilas a haramta amfani da maganin, kasancewar maganin tarin na Codeine ba magani ne da ya zama wajibi a yi amfani da shi wajen ceto rayuka ba, sai dai ma ya kasance daya daga cikin magungunan da ake amfani da su wajen sa maye a kasar.

Maganin na Codeine na ruwa yana jefa matasa da matan aure cikin halin ta'ammali da abubuwan dake sa maye a kasar, idan aka haramta amfani da maganin babu wata illa da hakan zai haifar wajen ceto rayukan jama'ar kasar, in ji Tambuwal.(Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China