in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gobara ta kone cibiyar raya al'adun gargajiya mafi girma ta Najeriya
2017-12-17 15:40:35 cri
Mahukunta sun tabbatar da cewa gobara ta yi mummunar barna a cibiyar fasaha da kayayyakin fasahar kirar hannu mafi girma ta Najeriya dake Abuja.

Kanayo Chimezie, shine shugaban kungiyar raya al'adun gargajiya na Afrika, ya bayyana cewa, gobarar ta tashi ne da yammacin ranar Juma'a, ta kone shaguna da dama da kuma kayayyakin fasahar gargajiya kirar hannu.

Chimezie yace, kawo yanzu ba'a gano musabbabin tashin gobarar ba.

A cewarsa, kayayyakin fasahar kirar hannu da shagunan da gobarar da lakume ya zarta dalar Amurka miliyan 1.1, saboda rashin zuwan jami'an kashe gobara wajen akan lokaci.

Mafi yawan kayan kirar hannun sababbi ne, kuma galibi an shirya su ne saboda bukukuwan karshen shekarar dake tafe, inji shugaban kungiyar raya al'adun gargajiyar.

Idan za'a iya tunawa a farkon watan Satumba ne, cibiyar raya al'adun gargajiyar ta Abuja ta karbi bakuncin babban taron baje kolin nune nunen kayayyakin fasahar gargajiya na Afrika.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China