Mai magana da yawun hukumar ta NAF, Olatokunbo Adesanya, ya fada cikin wata sanarwa wadda aka baiwa kofenta ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua a Legas cewa, hare haren da sojojin kasar suka kaddamar kan maboyar ya hallaka 'yan ta'addan dake boye cikinsu.
A cewarsa, jiragen saman yakin sojin saman 4 ne suka yi ta lugudan wuta a yankunan da 'yan ta'addan suka mamaye.
Adesanya ya fada cikin sanarwar cewa, dakarun tabbatar da tsaro na "LAFIA DOLE" sun killace yankin da mayakan suke samun mafaka, inda suka yi ta barin wuta a yankin na Kolaram, mai tazarar kilomita 37 dake gabashin Monguno a jahar Borno
Yace, binciken sirri da dakarun tsaron kasar suka gudanar a lokutan baya ne ya gano yankin Kolaram wanda 'yan ta'adda na Boko Haram ke amfani dashi a matsayin mafaka, kuma daga can ne suke shirya kai hare haren ta'addanci a sansanonin sojin kasar dake arewacin jahar Borno.