in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An samu rangwamen farashin mai a Nijeriya adaidai lokacin da ake neman tafiya yajin aiki
2017-12-19 10:53:00 cri
An warware matsalar farashin mai a Nijeriya, a daidai lokacin da dillalai ke ganin ma'aikatan bangaren mai za su shiga yajin aiki.

A jiya Litinin ne wata kungiyar ma'aikatan mai ta ce za ta janye daga tafiya yajin aikin gama gari, bayan ta samu biyan bukatunta ta hanyar sulhuntawa da Gwamnati da kuma wani kamfanin mai.

Yajin aikin ya haifar da damuwa game da fitar mai daga kasar da ta fi kowacce fitar da mai a nahiyar Afrika.

A daya bangaren kuma, cikin rahotonsa na mako, kamfanin mai na Baker Hughes dake Amurka, ya ce adadin na'urorin hakar mai a rijiyoyin man kasar sun ragu da guda 4 daga 747 dake akwai a makon da ya gabata, karon farko ke nan da aka samu raguwarsu cikin makonni 6.

Farashin Man da Kamfanin West Taxes ya samar don watan Janairu ya ragu da dala 0.14 inda ya tsaya kan dala 57.16 kan kowa ce ganga a kasuwar musaya ta New York, yayin da danyen man da Kamfanin Brent ya sayar domin watan Fabrairu ya karu da dala 0.18 inda ya tsaya kan dala 63.41 kan kowa ce ganga a kasuwar musaya ta ICE dake birnin London. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China