in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar zaben Nijeriya ta kuduri niyyar gudanar da sahihin zabe a shekarar 2019
2017-12-20 10:20:27 cri

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Nijeriya wato INEC, ta kara jaddada kudurinta na gudanar da sahihin zabe mai cike da adalci da zai karbu ga kowa a shekarar 2019.

Shugaban hukumar Mahmood Yakubu ne ya ba da tabbacin a jiya, yayin taro karo na hudu da masu ruwa da tsaki kan harkokin zabe, wanda hadakar kungiyoyin al'umma suka shirya a Abuja, babban birnin kasar.

Mahmood Yakubu ya ce, jam'iyyun siyasa 80 ne suka mika bukatar a yi musu rajista gabanin zabukan na shekarar 2019. Kuma a yanzu haka, akwai jam'iyyu 67 da aka riga an yi wa rajista a kasar.

Ya kara da cewa, ana ta neman hukumar ta yi 'yan takara masu zaman kansu rajista domin zabukan.

A cewarsa, yanzu haka suna tunanin yadda za su tsara takardar zabe, ta yadda za ta kunshi dukkan jam'iyyun da aka yi wa rajista, yana mai cewa hukumar za ta ba da muhimmanci na musammam ga yi wa masu zabe rajista.

Nijeriya dai ta shirya gudanar da babban zabenta ne a watan Fabrairun shekarar 2019. (Fa'iza Msutapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China