in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da hari kan jami'an shirin samar da abinci na MDD
2017-12-18 20:38:11 cri
Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da hari kan wata motar dakon kaya, ta jami'an shirin samar da abinci na MDD a jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya. Rundunar sojin dai ta danganta harin na ranar Asabar da kungiyar Boko.

Cikin wata sanarwa da aka fitar game da hakan, kwamanda dake jagorancin shirin lafiya dole mai yaki da Boko Haram a jihar ta Borno Manjo Janar Rogers Nicholas, ya tabbatar da aukuwar al'amarin, sai dai ya musanta cewa maharan sun hallaka fararen hula.

Ya ce sojoji sun yi arangama da mayakan kungiyar Boko Haram, inda nan take suka hallaka 6 daga cikin su, tare da kwato wasu makamai, amma ba wani farar hula da aka hallaka yayin artabun.

Sai dai a jiya lahadi ofishin shirin abinci na MDD ko (WFP) a takaice, ya ce ma an hallaka direban motar hayar da suka dauka aiki, da wasu mutanen su 3 a harin na Ngala dake karamar hukumar Gamboru-Ngala.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China