Kasar Morocco ta mika bukatar zama mamba a ECOWAS, yayin da kasar Tunisiya take neman kasancewa mai sanya ido a cikin kungiyar.
A taron kolin ECOWAS karo na 51 wanda ya gudana a birnin Monrovia, na kasar Liberia a watan Yuni, aka amince za'a duba bukatar kasar Moroccon na neman zama mamba a kungiyar.
Yayin da hukumar gudanarwar kungiyar ta sahhalewa kasar Tunisiya ta zama mai sanya ido.
Hukumar gudanarwar kungiyar ta kuma tabbatar da cewa, ta bukaci kasar Mauritania data gabatar da bukatarta na neman komawa kungiyar ta ECOWAS.
Shugaban kasar Mauritanian Mohamed Ould Abdel Aziz, da shugaban kasar Tunisiya Beji Essebsi, zasu gabatar da jawabai a matsayin baki na musamman a lokacin bude taron kolin.
Taron kolin zai kuma tattauna game da yanayin siyasa da tsaro da ake ciki a kasar Guinea Bissau.(Ahmad)