in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Najeriya ya amince da tsawaita wa'adin hafsoshin sojan kasar
2017-12-19 09:05:07 cri

Shugaba Muhammadu Buhari na kasar Najeriya ya amince da kara wa'adin manyan hafsoshin sojan kasar, musamman saboda irin gudummawar da suka ba da wajen yaki da mayakan Boko Haram da sauran matakan sojan da ake dauka a sassan kasar.

Ministan tsaron Najeriya Mansur Dan-Ali wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai jiya Litinin 18 ga wata, ya ce, shugaba Buhari ya kara wa manyan hafsoshin sojojin kasar wa'adin ne, bayan da ya nazarci tarin nasarorin da suka cimma ya zuwa wannan lokaci.

Ministan ya kara da cewa, shugaba Buhari musamman ya yi la'akari da rawar da manyan jami'an sojojin suka taka a yakin da ake yi da mayakan Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar da ma yanayin tsaro a yankin Niger Delta.

Dan-Ali ya ci gaba da cewa, kundin tsarin mulkin Najeriya, shi ne ya baiwa shugaban ikon kara wa manyan hafsoshin sojojin kasar wannan wa'adi.

Najeriya dai ta samu galaba a yakin da take yi da mayakan na Boko Haram, inda a farkon wannan shekara sojojin kasar suka yi nasarar fatattakar mayakan daga babban sansaninsu dake dajin Sambisa.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China