in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tankar mai ta yi bindiga a Lagos ta kone ababen hawa 20
2017-12-14 11:11:41 cri

Wata tankar dakon mai makare da man fetur ta yi bindiga a wata gada mai cunkoson jama'a a Legas cibiyar kasuwancin Najeriya, inda ta haddasa konewar motoci 20 da kuma babura 4 a jiya Laraba.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN, ya rawaito cewa, ba'a tabbatar ba ko gobarar wadda ta shafe sama da awa guda gabannin isar jami'an 'yan kwana-kwana zuwa inda lamarin ya faru, ko ta haddasa hasarar rayuka masu yawa ba.

Olufemi Popoola, wani da ya ganewa idonsa faruwar lamarin yace, tankar man ta yi yunkurin haurawa ta kan gadar ne dake garin FESTAC a Legas, amma daga bisani sai ta gangaro da baya kuma ta fadi.

A cewar Popoola, sanadiyyar rabuwar kan motar da tankin man ne ya haddasa fashewar tankar.

Wasu masu wucewa da mazauna yankin sun yi yunkurin kashe wutar ta hanyar amfanin da bokitan ruwa amma hakarsu bata cimma ruwa ba, kasancewar wutar dake ci a jikin tankar ta riga ta kama wasu ababen hawa dake daura da ita, abin da ya sanya masu ababen hawan suka gudu suka tsira da rayuwarsu.

Gobarar dai ta haddasa cunkoson ababen hawa a kan gadar wadda ta hada hanyoyi masu yawa.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China