in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta nanata matsayin ta na amincewa da kasar Sin daya tak a duniya
2017-12-15 09:15:37 cri

Mahukuntan Najeriya sun jaddada matsayin kasar game da amincewa da manufar kasar Sin daya tak a duniya, tare da tabbatar da cewa, yankin Taiwan bangare ne na kasar ta Sin, ba wata kasa mai cin gashin kan ta ba.

Wata sanarwa da ofishin sakataren gwamnatin Tarayyar Najeriyar ya fitar, wadda kuma aka rabawa ma'aikatu, da hukumomin gwamnatin kasar, ta jaddada kasancewar birnin Beijing a matsayin fadar mulkin kasar. A don haka ne ma shugaban Tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari, ya bada umarnin dakatar da bayyana "Jamhuriyar Sin" tare da Taiwan, cikin duk wasu huldodi da suka shafi ayyukan gwamnati.

Kaza lika an bukaci dukkanin jami'an gwamnatin Najeriyar dake son gudanar da wata ziyara ta kashin kai zuwa yankin Taiwan, da su nemi izini daga ofishin sakataren gwamnatin kasar.

Sanarwar ta kuma nanata kudurin gwamnatin Najeriya, na ci gaba da fadada kyakkyawar alakar dake tsakanin kasar da Sin.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China