Kwamda mai barin gado na rundunar Operation lafiya Dole mai yaki da kungiyar Boko Haram wato Ibarhim Attahiru, shi ne ya bayyana haka ga manema labarai jiya a birnin Maiduguri, inda ya ce ana samun galaba akan mayakan, domin rundunar sojin ta yi nasarar kwato dukkan yankunan dake hannun kungiyar.
Ibrahim Attahiru, ya ce rundunar ta kaddamar da ayyuka daban-daban dake da nufin murkushe 'yan ta'addan tare da tabbatar da dorewar nasarar da aka samu na yaki da ta'addanci.
Da farko, sabon Kwamandan da zai ja ragamar rundunar Operation Lafiya Dole Rogers Nicholas, kira ya yi ga mayakan Boko Haram su ajiye makamai su rungumi zaman lafiya.
Ya ce abu ne mai muhimmanci gaya, karfafawa ragowar 'yan ta'addan gwiwar mika wuya, domin samar da zaman lafiya mai dorewa a yankin. (Fa'iza Msutapha)