in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya na fatan bunkasa zuba jari a fannin makamashi da ake sabuntawa
2017-12-14 11:14:46 cri

Ministan ma'aikatar kimiyya da fasaha a Najeriya Ogbonnaya Onu, ya ce kasar sa na fatan bunkasa hada hadar zuba jari a fannin makamashi da ake iya sabunta amfani da shi, a wani mataki na ingiza ci gaban masana'antun kasar.

Wata sanarwa da aka fitar ta rawaito ministan na cewa, sashen makamashi da ake sabuntawa na tattare da riba maras iyaka, kuma gwamnatin Najeriya na daukar matakan kau da dukkanin kalubale dake hana ruwa gudu wajen ci gaban sa.

Ya ce yanzu haka ana kokarin samar da dokoki da suka wajaba, wadanda za su share fage ga kudurin cimma gajiyar da ta kamata a fannin. Mr. Onu ya kara da cewa, kawo yanzu Najeriya ba ta cin cikakkiyar gajiya, daga sashen samarwa, da sarrafa makamashi da ake iya sabuntawa.

Ministan ya kara da cewa, shigar da fannin makamashi da ake iya sabuntawa cikin bukatun makamashi da ake da shi a Najeriya, zai fadada guraben ayyukan yi, da rage talauci, tare da taimakawa al'ummar kasar samun karuwar wadata.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China