in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Najeriya ya bukaci a gudanar da hulda mai tsabta a nahiyar Afrika
2017-12-17 12:45:44 cri
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya bukaci a gudanar da mu'amala bisa gaskiya da kyakkyawar makwabtaka a tsakanin shiyyoyi da yankunan nahiyar Afrika.

Shugaban ya yi wannan kiran ne a wata sanarwa da aka fitar bayan ganawa da shugaban kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS, Marcel A. De Souza a Abuja, babban birnin kasar.

Shugaba Buhari ya yabawa shugabancin kungiyar ECOWAS bisa bukatar data gabatar na neman bindiddigin yadda kungiyar ke tafiyar da al'amurranta, inda hakan ya sanya ta gayyaci hukumar yaki da rashawa ta Najeriyar (EFCC) data binciki asusun ajiyar kudadenta.

Buhari yace Najeriya zata cigaba da sauke dukkan nauyin dake wuyanta na jagorancin kungiyar a tsakanin shiyyoyin nahiyar.

A ranar 16 ga watan nan na Disamba ne Najeriya ta karbi bakuncin taron koli na ECOWAS karo 52.

Shugaban Buhari yace yana jiran karbar rahoto game da halin da ake ciki a Guinea Bissau a yayin wannan taron.

Ya kara da cewa, suna bukatar dakarun da aka tura kasar su dawo gida, kuma suna fata shugaban kasar ta Guinea Bissau zai amince da bin hanyoyin da tsarin mulkin kasar ya tanada wajen warware halin tsaron da kasar ke fuskanta. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China