in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Arewa maso gabashin Najeriya na matukar bukatar tallafin jin kai, in ji wani jami'in MDD
2017-12-12 10:31:00 cri
Jami'in tsare tsare a ofishin MDD mai kula da ayyukan jin kai ko OCHA a takaice Edward Kallon, ya ce arewa maso gabashin Najeriya na cikin yankuna dake sahun gaba, wajen bukatar tallafin jin kai a duniya.

Mr. Edward Kallon, ya bayyana hakan ne a birnin Maiduguri, fadar mulkin jihar Borno a jiya Litinin. Ya ce a halin da ake ciki, MDD ta ware kudi har dalar Amurka miliyan 13.4, domin ayyukan da ofishin ta na bada tallafin jin kai dake Najeriyar ko NHF a takaice zai aiwatar.

Ana dai fatan amfani da kudaden ne wajen agazawa sama da mutane miliyan 1 dake da matukar bukatar agaji a yankin da ya sha fama da tashe tashen hankula masu nasaba da ayyukan kungiyar Boko Haram.

Jami'in ya kara da cewa, a bana kadai, mutane da yawan su ya kai miliyan 8.5 na matukar bukatar tallafin gaggawa, domin fita daga matsananciyar rayuwa a jahohin Borno, da Adamawa da Yobe, jahohin da suke kan gaba wajen fuskantar wannan matsala.

Mr. Kallon ya ce kudaden da aka ware ga ofishin na NHF, za su taimaka wajen daukar matakan dakile matsaloli mafiya tsanani dake addabar wannan yanki, karkashin wasu ayyuka 24 da za a gudanar, ciki hadda na samar da abinci mai gina jiki, da tsaftacaccen ruwan sha, da tsaftar muhalli, da kiwon lafiya da kuma samar da ilimi. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China