Wannan ya biyo bayan karewar wa'adin wadanda aka zaba shekaru 5 da suka wuce, ciki har da Shugaban Jam'iyyar kuma shugaban kasa Jacob Zuma. An zabi wandanda za su yi takarar ne yayin babban taron Jam'iyyar ANC karo na 54 dake gudana a birnin Johannesburg.
Jam'iyyar ta zabi mataimakin shugaban kasar Cyril Ramaphosa da tsohuwar shugabar hukumar kula da Tarayyar Afrika Nkosazana Dlamini-Zuma, a matsayin wadanda za su yi takarar shugabancinta. Rassan jam'iyyar 1,469 daga larduna 6 na kasar ne suka zabi Cyril Ramaphosa, yayin da rassa 1,094 daga larduna 6 suka zabi Nkosazana Zuma.
An kuma zabi David Mabuza da Lindiwe Sisulu a matsayin wadanda za su takarar mukamin mataimakin shugaban Jam'iyya.
Ana sa ran sanar da sakamakon zaben a yau Litinin, kuma ba za a bayyanawa kafafen yadda labarai tsarin zaben ba.
Taron zai kuma zabi mambobin majalisar zartarwar jam'iyyar 80. (Fa'iza Mustapha)