Fadar gwamnatin ta bakin kakakinta Bongani Ngqulunga, ta ce shugaban kasar Jacob Zuma ne zai sanya hannu kan yarjejeniyar a madadin kasarsa a ranar Laraba mai zuwa.
Manufar hakan dai ita ce, tabbatar da kasar na amfani da sinadaran nukiliya da take sarrafawa ta hanyoyin da ba su shafi samar da makaman kare dangi ba.
Rahotanni na cewa, shugaba Zuma zai isa birnin New York, domin halartar babban taron MDD, wanda aka yiwa lakabi da "Mai da hankali kan al'umma: kokari domin wanzar da zaman lafiya da managartaciyar rayuwa ga kowa domin duniya mai inganci".
Wannan ne karon farko da MDDr za ta yi babban zaman muhawara, tun bayan da babban magatakardanta na yanzu Antonio Guterres ya kama aiki a ranar 1 ga watan Janairun bana. (Saminu Hassan)