Shugaban jam'iyyar ANC na yanzu, kuma shugaban kasar Afirka ta kudu, Jacob Zuma ya bayar da rahoto kan yadda ya gudanar da ayyukansa, inda ya bayyana cewa, yanzu kasarsa na fuskantar tabarbarewar tattalin arziki, don haka akwai bukatar kawar da talauci, da kyautata rashin daidaito, da kuma kara samar da guraban ayyukan yi ga jama'ar kasar.
Baya ga haka, Zuma ya ce, ko da yake jam'iyyar ANC na fuskantar kalubaloli da dama, amma tana samun amincewa daga wajen yawancin jama'ar kasar. A cewarsa, dole ne jam'iyyar ta bada jagoranci wajen neman hanyar warware matsalolin da kasar ke fuskanta.
An yi hasashen cewa, za a zabi sabon shugaban jam'iyyar ta ANC ne a safiyar ranar 17 ga wata bisa agogon wurin, don maye gurbin shugaban na yanzu Jacob Zuma, amma shugaba Zuman zai ci gaba da zama a kujerar shugaban kasar Afirka ta kudu har zuwa lokacin babban zaben kasar a shekarar 2019. (Bilkisu)