Gwamnatin kasar ta bayyana haka ne bayan hukumar dake auna karfin bashi wato kamfanin Standard and Poor's ya dauki matakin rage matsayin damar biyan bashin da kasar keda shi.
Gwamnatin ta bayar da sanarwa cewa, kwamitin kula da harkokin kudi na kasar wanda ke karkashin jagorancin shugaba Jacob Zuma na kasar, zai yi kokarin maido da kasuwanci da imanin masu sayen kaya, kana da gudanar da manufar ci gaban tattalin arziki da ta tsara a baya, musamman ma a fannin rage kudin da gwamnatin ke kashewa.
A ranar 24 ga wata, kamfanin Standard and Poor's ya sanar da rage matsayin damar iya biyan bashin kasar Afirka ta kudun, bisa dalilan samun tabarbarewar harkokin kudin jin dadin al'umma sakamakon rashin saurin ci gaban tattalin arzikin kasar.
A nasa bangaren, Kamfanin Moody's dake auna karfin bashi ya yi gargadin cewa, zai yi bincike kan Afirka ta kudu na kwanaki 90, daga baya sai ya tsaida kuduri kan ko zai rage matsayin iya biyan bashin ko a'a.
A ganin kamfanin, kalubalen da kasar ke fuskanta a fannin tattalin arziki da kudi yafi tsanani bisa yadda aka yi hasashe, yana nuna damuwa game da makomar tattalin arzikin kasar. (Bilkisu)