Jacob Zuma ya ce sauyin zai tabbatar da iko da kula da tattalin arziki ba shi da alaka da launin fata, tare da tabbatar da bai kasance hannun fararen fata ba kadai.
Shugaban ya bayyana haka ne a jiya, a sakonsa na bikin ranar al'adu da aka sadaukar ga dimbin al'adun gargajiya na kasar, inda ya gudanar da bikin tare da al'ummar Siyabuswa dake lardin Mpumalanga.
Jacob Zuma ya yi amfani da ranar wajen bayyana burinsa na sauya tsarin tattalin azriki da zamantakewa tun daga tushe, a daidai lokacin da ake tsaka da korafi tsakanin bakaken fata dake cewa, akwai bukatar karfafa musu ta fuskar tattalin arziki la'akari da rinjayensu. (Fa'iza Mustapha)