in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zuma zai kafa tsarin kasuwanci marar shinge a Afrika
2017-10-10 10:44:08 cri
Shugaban kasar Afrika ta kudu Jacob Zuma ya sanar a ranar Litinin cewa, kasarsa za ta kafa tsarin kasuwanci mai 'yanci na nahiyar Afrika wato (CFTA), kamar yadda kungiyar tarayyar Afrika AU ta jima tana mafarkin tabbatar da hakan.

Zuma ya bayyana hakan ne a lokacin da yake amsa tambayoyi a gaban majalisar dokokin kasar cewa, Afrika ta kudu ta dauki batun cimma matsaya na kafa tsarin na CFTA da matukar muhimmanci, kana kasar tana fatar kafa wannan tsari zai samar da kyakkyawar makoma ga bunkasuwar tattalin arziki da ci gaban nahiyar Afrika.

A shekarar 2012 ne AU ta yanke shawarar kafa CFTA zuwa watan Oktoban shekarar 2017, kuma an sake jaddada wannan aniyar a watan Nuwambar shekarar 2016 a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha.

Manufar kafa wannan tsarin shi ne, domin samun damar karfafa tsarin cinikayya tsakanin shiyyoyi da kuma bada damar aiwatar da kasuwanci tsakanin kasashen nahiyar Afrika ba tare da samun tangarda ba. Batun kafa tsarin cinikayya mai 'yancin, yana daga cikin babbar ajandar bunkasuwar ci gaban kasashen Afrika nan da shekarar 2063 wanda kungiyar AU ta kafa.

Shugaba Zuma ya ce, kasar Afrika ta kudu ta samu babban ci gaba game da kafa tsarin kasuwanci mai 'yanci wato CFTA, wanda ya kunshi bunkasa kasuwanni, da masana'antu, da ci gaban ababan more rayuwa. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China