in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mataimakin shugaban kasar Afrika ta kudu ya bukaci matasa su zama masu da'a
2017-10-08 12:55:04 cri
Mataimakin shugaban kasar Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa, kuma mataimakin shugaban jam'iyyar ANC mai mulkin kasar, ya bukaci matasan jam'iyyar da su kasance masu da'a da hangen nesa.

Ramaphosa ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a gaban gamayyar matasan kungiyar ANCYL, a Johannesburg domin bikin murnar cika shekaru 73 da kafa kungiyar.

Ya ce kamata ya yi matasan su mayar da hankali wajen zaburar da al'ummar domin samun kyakkyawar makoma a nan gaba. Kamata ya yi matasan su yi watsi da duk wani abun da ba zai amfanar da su a rayuwarsu ba. Kamata ya yi matasan su guji aikata duk wani abu na rashin da'a, da cin zarafin jama'a. Ya ce a matsayinsu na matasa kada su yi sakaci wani abu ya dauke musu hankali ko kuma ya haifar da rarrabuwar kawuna a tsakaninsu. Ya ce dole ne su dauki matakai na kare martabar jam'iyyar ANC mai mulkin kasar.

Ramaphosa ya ce, ya kamata matasan su yi aiki tukuru wajen karfafa jam'iyyar kuma su tabbatar da ganin jam'iyyar ta ANC ta samu cikakken karfi kamar yadda shugabanninta na asali suka assasata.

Ya kara da cewa, ya kamata matasan su mayar da hankali wajen yin ilmi, kuma su ba da himma wajen nazartar fannin da za su samu kwarewa wadanda kasar take da matukar bukata a halin yanzu. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China