in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Burundi za ta gudanar da zaben raba gardama kan gyaran kundin tsarin mulki a watan Mayun badi
2017-12-16 12:36:48 cri

Hukumar zaben kasar Burundi mai zaman kanta wato CENI, ta ce zaben raba gardama kan gyaran kundin tsarin mulkin kasar dake gabashin Afrika, zai gudana cikin watan Mayun badi.

Shugaban hukumar CENI Pierre Claver Ndayicariye ne ya bayyana haka, yayin wani taron masu ruwa da tsaki kan harkokin zabe da suka hada da wakilan jam'iyyun siyasa da na kungiyoyin al'umma da kungiyoyin addini, wanda ya gudana jiya Jumma'a a birnin Bujumbura.

Pierre Claver Ndayicariye ya ce, sun shirya gudanar da zaben raba gardamar a watan Mayu mai zuwa, sai dai za a sanar da ainihin ranar ne a lokacin da fadar shugaban kasa ta rattaba hannu kan umarnin sanar da ranar.

Daftarin kundin tsarin mulkin kasar da za a yi zaben raba gardama kansa, bai tanadi haramtawa shugaba Nkurunziza neman sake tsayawa takara ba.

Sai dai ya tsawaita wa'adin mulki daga shekaru 5 dake kunshe cikin kundin tsarin shekarar 2015 zuwa shekaru 7, sannan ya bai wa shugaban kasa damar yin wa'adin mulki har sau biyu a jere. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China