Hukumar TRC mai binciken muggan abubuwan da gwamnatocin baya suka yi tare da warware rikice-rikicen da aka yi gado ta kasar Burundi, ta gano kaburburan jama'a sama da 110 a lardin Mwaro dake tsakiyar kasar.
Shugaban Hukumar Monsignor Jean Louis Nahimana, ya ce kididdigar da aka yi kan kaburburan na Mwaro ta nuna cewa, kisan kiyashin da aka yi a kasar cikin shekarar 1972 da 1993 ya bar kaburburan jama'a sama da 110 a yankuna daban-daban na lardin.
Ya ce mazauna yankin ne suka nuna musu inda kaburburan suke, amma sai da suka tantance kafin su aminta da su.
Monsignor Nahimana ya bukaci hukumomi a lardunan Mwaro da Karusi su kare shaidar kaburburan, domin akwai wasu bata gari da za su yi kokarin boye shaidar ayyukan muguntar. (Fa'iza Mustapha)