in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Minista: matsalar makamashi a Burundi na gab da zuwa karshe
2017-06-09 13:23:44 cri

Ministan makamashi da ma'adanai na kasar Burundi Come Manirakiza, ya ce matsalar makamashi da kasar ke ciki wata da watanni, na gab da zuwa karshe.

Come Manirakiza, ya ce duk da ba zai iya fadin hakikanin lokacin ba, amma nan ba da dadewa ba, za a samu isasshen wutar lantarki a kasar, ya na mai cewa, ba za a kuma samun rahoton lodin lantarki fiye da kima ba, saboda za a samu wadatuwar lantarkin.

A cewarsa, a mako mai zuwa ne za a fara taron da ke da nufin kammala shirye-shiryen aikin bunkasa samar da makamashi, sai dai, bai yi karin bayani game da aikin ba.

Har ila yau, ministan ya shawarci al'ummar kasar da ke shirin sayen injin Janerata a matsayin mafita wajen samun lantarki a gidajensu da wuraren sana'o'i, da su kauracewa yin hakan, ya na mai alkawarin cewa, za a samu wadatuwar wutar cikin kankanin lokaci.

Come Manirakiza, ya kuma bayyana cewa, za a samu karuwar farashin lantarki kadan, inda ya jadadda cewa, binciken da aka gudanar a baya-bayan nan ya nuna a shirye wasu mazauna suke, su saye lantarkin kan farashi mai tsada maimakon rasa shi baki daya. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China