Kungiyar EAC dai na kunshe da kasashe shida da suka hada da Burundi, da Kenya, da Rwanda, da Tanzania, da Afirka ta kudu da kuma Uganda. Sai dai kuma kawo yanzu, ba ta kai ga zama ta siyasa ba, matakin da shi ne na karshe a matakan dunkulewar kasashen dake cikinta.
Shugaba Nkurunziza, ya bayyana cewa babban kalubalen da EAC ke fuskanta shi ne na hade sassan kungiyar, ta yadda za a kai ga cimma nasarar dunkule kasashen dake karkashin ta wuri guda. (Saminu Hassan)