Shugaba Nkurunziza ya kaddamar da hanyar ne a jiya Alhamis, kuma rahotanni sun tabbatar da cewa tsawon ta ya kai kilomita 44.5, za ta kuma hade yankunan al'ummun dake arewa maso gabashin Mugina, da birnin Nyanza Lac mai makwaftaka da Makamba.(Saminu Alhassan)