in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mahukuntan Burundi sun bukaci da a tantance masu neman mafaka
2017-08-22 09:20:14 cri
Ministar ma'aikatar shari'a ta kasar Burundi Aimee Laurentine Kanyana, ta bukaci tsohon shugaban kasar Tanzania Benjamin Mkapa, da ya jagoranci binciken dalilan da suka sanya wasu 'yan kasar ta kin komawa gida, duk da cewa yanzu haka hankula sun kwanta a kasar ta Burundi.

Uwar gida Kanyana, ta yi wannan kira ne yayin zantawar ta da Mr. Mkapa, wanda ke ziyarar aiki a Burundi. Da take yiwa kamfanin daillancin labarai na Xinhua karin haske game da kiran da ta yi, Kanyana ta ce, tana fatan Mr. Mkapa wanda ke jagorantar tawagar masu shiga tsakani karkashin kungiyar hadin kan gabashin Afirka ta EAC, da hadin gwiwar gwamnatin Burundi, za su yi tsayin daka wajen tantance dalilan da suka sanya wasu 'yan kasar ta, ci gaba da neman mafaka a sansanonin 'yan gudun hijira dake ketare.

Ministar ta kara da cewa, wasu daga 'yan kasar na tserewa ne sakamakon rigingimu na iyalai, ko saboda sun aikata manyan laifuka kamar fashin banki, ko sun ci bashin bankuna da suka gagare su biya, yayin da kuma wasu ke fakewa a kasashen ketaren domin samun damar tsallakawa turai ta barauniyar hanya.

Mr. Mkapa da 'yan tawagar sa dai na ziyara ne a Burundi, tsakanin ranekun 14 zuwa 19 ga watan nan na Agusta. Kuma makasudin ziyarar ta su a Burundi shi ne jan ra'ayin mahukuntan kasar, game da bukatar hawa teburin shawara da bangarorin kasar wadanda ba sa ga maciji da juna, ta yadda za a kai ga warware takaddamar siyasa, wadda ke neman dagula al'amuran kasar.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China