in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar dokokin Burundi ta soki shawarwarin UNHRC game da take hakkin dan adam
2017-10-03 13:42:22 cri

A ranar Litinin majalisar dokokin kasar Burundi ta yi Allah wadai da shawarwarin da hukumar kare hakkin bil adama ta MDD (UNHRC) ta bayar, inda ta bada umarnin a sake kafa kwamitin da zai binciki laifukan take hakkin dan adam a kasar Burundin tun daga shekarar 2015.

A makon jiya ne, hukumar UNHRC ta amince da wani kuduri inda ya tsawaita wa'adin hukumar bincike da shekara guda, don binciko laifukan taken hakkin bil adama da aka aikata a kasar ta Burundi.

MDD ta nada masu bincike na UNHRC guda 3 a watan Satumba, inda ta gabatar da wani rahoto wanda ya nemi kotun hukunta laifukan yaki ta kasa da kasa ICC da ta bude tuhumar nan da ake zargin gwamnatin Burundi na take hakkin dan adam tun daga shekarar 2015.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China