Yau Alhamis ne, madam Hua Chunying, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana a yayin taron manema labaru cewa, takaddamar dake tsakanin kasashen Koriya ta Arewa da Amurka shi ne dalilin da ya ta'azzara hali da ake ciki a zirin Koriya. Haka kuma kasashen biyu ba su amince da juna ba, musammam ma a fannin tsaro. Hanya daya kacal da za a iya bi wajen warware wannnan matsala ita ce biyan bukatun sassa daban daban yadda ya kamata ta hanyar yin tattaunawa da shawarwari. (Tasallah Yuan)