in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na fatan Koriya ta Kudu za ta cika alkawarinta
2017-10-31 19:39:45 cri

Yau Talata ne madam Hua Chunying ta ce, daidaita batun girke na'urorin kakkabo makamai masu linzami samfurin THAAD yadda ya kamata, da kau da duk shinge dake kawo cikas ga huldar da ke tsakanin Sin da Koriya ta Kudu, shi ne burin kasashen 2, wanda kuma ya dace da muradunsu.

Yau da safe ne, kasashen Sin da Koriya ta Kudu suka sanar da sake tuntubi juna ta fuskar huldar da ke tsakaninsu.

A yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan Beijing, an yi tambayar cewa, ko kasar Sin za ta sauya matsayinta kan batun girke na'urorin kakkabo makamai masu linzami samfurin THAAD bayan da kasashen 2 suka tuntubi juna. Madam Hua ta ce, kasar Sin ba za ta sauya matsayinta kan wannan batu ba. Kasar Sin ta lura da cewa, Koriya ta Kudu ta fito fili ta nuna cewa, ba za ta shiga tsarin kakkabo makamai masu linzami da kasar Amurka ke jagoranta ba. Kana ba za ta fadada hadin gwiwar da ke tsakaninta da Amurka da Japan a fannin soja ba. Haka kuma ba za ta kara girke na'urorin kakkabo makamai masu linzami samfurin THAAD ba. Sa'an nan wadannan na'urori da aka girke a Koriya ta Kudu ba za su kawo wa kasar Sin illa ta fuskar tsaro ba. Kasar Sin na fatan Koriya ta Kudu za ta aiwatar da abun da ta furta a zahiri. Sannan za ta daidaita batutuwa dake da nasaba da wannan lamari kamar yadda ya kamata. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China