Rahotanni na cewa kasar Amurka ta tsara wani sabon daftarin doka, game da shirin sanya wa kasar Koriya ta Arewa takunkumi, sakamakon gwajin makaman nukiliya da Koriya ta Arewa ta yi karo na 6. Yanzu haka dai mahukuntan Amurka za su mika daftarin dokar ga kwamitin sulhu a Litinin din nan domin kada kuri'a.
Dangane da hakan, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya jaddada a yau Litinin cewa, kasar Sin na maraba da matakin da kwamitin sulhu zai dauka, sai dai fa dole ne matakin ya taimaka wajen tabbatar da raba zirin Koriya da makaman nukiliya, da tabbatar da wanzuwar zaman lafiya da kwanciyar hankali a zirin, da kara azama kan warware batun nukiliyar zirin cikin ruwan sanyi kuma a siyasance. (Tasallah Yuan)