in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin kiyaye zaman lafiya na MDD sun harbe dakarun kungiyar adawa da gwamnatin Uganda sama da guda 70
2017-12-10 13:40:32 cri
Kakakin rundunar sojan kasar Congo-kinshasa ya sanar a ranar 8 ga wata cewa, sojojin kiyaye zaman lafiya na MDD sun harbe mayakan kungiyar adawa da gwamnatin kasar Uganda ADF, sama da guda 70, a harin da dakarun suka kai a daren ranar 7 ga wata.

Kakakin ya kara da cewa, a daren ranar 7 ga watan, mayakan kungiyar ta ADF sun kai hari kan sojojin kiyaye zaman lafiya na MDD dake lardin arewacin Kivu dake gabashin kasar Congo-kinshasa, inda sojojin kiyaye zaman lafiyar MDD suka harbe mayakan kungiyar a kalla 72.

Haka kuma, bisa wata sanarwar da kwamitin sulhu na MDD ya fitar a ranar 8 ga wata, an ce, harin da aka kai ya haddasa rasuwar sojojin kiyaye zaman lafiya na MDDr 'yan kasar Tanzania su 15, sannan a kalla sojoji 53 ne suka jikkata. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China