An tsaurara matakan tsaro a Kampala yayin da majalisar dokokin Uganda ke shirin bayyana shekarun tsayawa takarar shugabancin kasar
Rahotanni daga Kampala, babban birnin kasar Uganda, na cewa, yanzu haka an tsaurara matakan tsaro a ciki da wajen birnin, a wani mataki na magance duk wani tashin hankali da ka iya barkewa, yayin da majalisar dokokin kasar ke shirin soke adadin shekaru 75 ga mai neman tsayawa takarar shugabancin kasar.
Kakakin rundunar 'yan sandan kasar Asan Kasingye, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, an girke sojoji da 'yan sanda a Kampala, musamman harabar majalisar dokokin kasar da sauran muhimman wurare da ma manyan garuruwan kasar. (Ibrahim)