Birgediya Richard Karemire, shi ne mai magana da yawun rundunar sojin kasar Uganda ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, mayakan 'yan tawayen kasar Uganda ADF, sun kasance suna boye ne a gabashin kasar DRC, ya ce dole ne a bankado su don murkushe su.
A daren Alhamis da ta gabata, 'yan tawayen sun kaddamar da hari a lardin Kivu na arewacin DRC inda suka raunata dakarun wanzar da zaman lafiya 53.
A cewar Karemire, mayakan ADF sun kasance babbar barazana ga zaman lafiyar da kwanciyar hankalin yankin. Ya ce daukar matakan kawar da 'yan ta'addan a gabashin DRC shi ne babban aikin dake gaban gwamnatin Kinshasa.
Ya ce dakarun wanzar da tsaro na kasar Uganda UPDF, za su ci gaba da kare kan iyakoki don kaucewa kwararar 'yan tawayen a sassan kasar.
Wasu alkaluma da MDD ta fitar ya nuna cewa, tun lokacin da aka kafa tawagar kiyaye zaman lafiya ta MDDr a DRC a shekarar 2010, ta yi hasarar dakarun soji 93, da 'yan sanda, da kuma jami'an sa-kai na fararen hula. (Ahmad Fagam)