Shugaban majalisar dokokin kasar Sin Zhang Dejiang ya gana da takwararsa ta Uganda Rebecca Kadaga jiya a nan birnin Beijing, inda suka amince da zurfafa musayar bayanai da hadin gwiwa kan ayyukan majalisunsu.
Zhang Dejiang wanda shi ne shugaban kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin wato NPC, ya ce dangantakar dake tsakanin kasar Sin da Uganda ya samu tagomashi a shekarun baya-bayan nan karkashin jagorancin shugabannin kasashen biyu.
Ya ce a shirye kasar Sin take ta inganta hadin gwiwa da Uganda a fannonin da suka hada da samar da kayayyakin more rayuwa da makamashi da ma'adinai da masana'antu da kuma noma.
Har ila yau, ya ce Sin na mara baya tare da karfafa gwiwar kamfanoninta wajen zuba jari a Uganda, kuma tana fatan Uganda za ta taimakawa kamfanonin wajen warware matsalolin da suke fuskanta karkashin hadin gwiwar.
Zhang Dejiang ya ce a shirye kasar Sin take ta yi musayar dabarunta da Uganda a fannonin shugabanci da dokoki, musammam bangaren dokoki domin bunkasa ci gaban kanana da matsakaitan sana'o'i da jan hankalin masu zuba jari na kasashen ketare.
A nata bangaren, shugabar majalisar dokokin Uganda Rebecca Kadaga, ta ce ziyarar da ta kawo wa kasar Sin, ya kara mata fahimta game da kasar, inda ta ce majalisar dokokin Uganda ta dauki dangantakar dake tsakanin kasashen biyu da muhimmanci, kuma a shirye take ta yi aiki da NPC wajen zurfafa hulda a bangarorin noma da noman rani da ilimi da kare muhalli.
Ta kuma kara da cewa, Uganda na maraba da masu zuba jari na kasar Sin.(Fa'iza Mustapha)