Aikin shimfida bututun man na shiyyar gabashin Afrika (EACOP) mai tazarar kilomita 1,443, zai kashe kudi kimanin dalar Amurka biliyan 3.55, idan aikin ya kammala, za'a rika tura litar mai dubu 200 a kullum. Kana zai kasance bututun mai dake amfani da lantarki mafi tsawo a duniya.
Hukumomin sun bayyana cewa aikin na EACOP zai kankama ne a farkon shekarar 2018, kuma za'a dauki tsawon watanni 36 kafin a kammala shi, wanda kuma ake sa ran zai samar da guraben aikin yi tsakanin dubu 6 zuwa dubu 10.
Da yake jawabi a lokacin kaddamar da shirin mai matukar tarihi, wanda ya samu halartar dubban mutane daga kasashen na gabashin Afrika biyu, Magufuli ya bayyana aikin da cewa wani mataki ne wanda zai samar da cigaba ga kasashen biyu har ma da shiyyar gabashin Afrika gaba daya.
A nasa bangaren Museveni, ya bayyana cewa aikin zai taimaka wajen rage tsadar farashin man fetur, kuma zai bunkasar kamfanin sufurin jiragen sama, inda za'a dinga samun man jirgin a farashin mai rahusa.(Ahmad Fagam)