in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
WHO na kokarin dakile wata kwayar cuta ta dangin Ebola a iyakar Uganda da Kenya
2017-10-21 13:43:08 cri
Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta ce ta na kokarin yaki da wata matsananciyar kwayar cuta mai hadari ta dangin Ebola a yankin gabashin Uganda dake iyaka da Kenya.

Kwayar cutar Marburg wato MVD a takaice, cuta ce mai kisa da ba a saba gani ba, wadda kuma ba ta da magani takamaimai. Sannan ta na daga cikin kwayoyin cuta masu hadari dake kama bil adama, inda take farawa da alamomin da suka hada da zazzabi da ciwon kai da jin sanyi da da kuma ciwon damatsa.

WHO ta ce akalla mutum guda ne aka tabbatar da mutuwarsa sanadiyyar cutar, yayin da daruruwa ke cikin barazanar kamuwa da ita a asibitoci da taron jana'iza na gargajiya a lardin Kween, mai tsaunuka dake da nisan kilomita 300 daga kudu maso gabashin Kampala, babban birnin Uganda.

An gano bullar cutar ta farko ne a ranar 17 ga watan Oktoba, inda wata mata mai shekaru 50 ta mutu a wani asibiti, bayan ta yi fama da zazzabi da zubar jinni da amai da gudawa, kuma gwajin da aka yi a ranar 11 ga wata a cibiyar binciken kwayoyin cuta ta Uganda, ya nuna cewa kwayar cutar MVD ce ta haddasa mutuwar.

Shi ma wani dan uwan matar ya mutu bayan yayi fama da alamomin cutar, makonni uku kafin mutuwar matar, inda aka mishi jana'iza irin ta gargajiya.

Mutumin mafarauci ne dake zama a wani kogo da ya kasance muhallin jemagu, wadanda su ne asalin masu dauke da kwayar cutar Marburg.

Hukumar WHO ta ce ana bincike akan wasu mutane 2 da ake zargin sun kamu da cutar inda kuma ake kula da lafiyarsu. Sannan ana gudanar da bincike kan wasu mutanen da ake tunanin sun kamu da cutar ko kuma suke cikin hadarin kamuwa da ita. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China